<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>10</hymn_number>
<title>Muna Son Wurin Nan Na Darajar Allah LW10</title>
<lyrics>[V1]
 1) Muna son wurin nan na darajar Allah.
 Murna ta ɗakin na ta fi a kwatanta.

[V2]
 2) Ɗakin addu'a ne na taron bayinka.
 Lalle fa kana nan tare da jama'a.

[V3]
 3) Wurin Baftisma fa mu ke sonsa ƙwarai,
 Gama nan Ruhunka ke ba da alherai.

[V4]
 4) Muna son Tebur ma, wuri ƙaunatacce.
 Nan ka ke ciyad da mu cikin bangaskiya.

[V5]
 5) Maganarka ta rai, ita ma mu ke so.
 Ta ba da kwanciyar rai, salama ta kan kawo.

[V6]
 6) Yanzu mu ke ta yin waƙa ta jinƙanka,
 Amma can Sama fa da waƙar nasara.

[V7]
 7) Ya Yesu, ƙara dai alheri da ƙauna
 Ga mu jama'arka, mu dinga sujada.</lyrics>
</song>